EDITA.

A wani lamari mai tayar da hankali da ya auku a jihar Odisha da ke ƙasar Indiya, an samu wani mutum mai shekaru sama da 50 da ya haƙo gawar ’yar’uwar sa daga kabarin ta tare da kai ta banki domin ƙoƙarin tabbatar da cewa ta rasu, domin a ba shi damar cire kuɗi daga asusun ta.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya yi wannan abin mamaki ne bayan bankin ya ƙi amincewa da maganganun sa na cewa ’yar uwar sa ta mutu, duk da cewa a baya an riga an sanar da bankin rasuwar ta.

Majiyoyi sunce lamarin ya faru ne bayan mutuwar matar a watan Janairun wannan shekara, inda daga bisani ɗan’uwan ta ya tunkari banki domin cire kuɗin da ake zargin ya kai rupee dubu 20 (kimanin dala 200).

Sai dai rashin amincewar bankin da bayaninsa ya sa lamarin ya rikide zuwa abin da ya janyo cece-kuce, inda daga bisani aka samu rahoton cewa ya tono gawar daga kabari domin kai ta a matsayin hujja.

Hukumomin tsaro a yankin sun shiga bincike domin gano cikakken bayanin abin da ya faru, yayin da al’umma ke ci gaba da nuna mamaki da rashin fahimtar dalilin da ya kai ga wannan mataki mai ban tausayi da kuma ban mamaki.

Wannan lamari ya kara jawo tambayoyi kan yadda ake tabbatar da bayanan mutuwa da kuma hanyoyin da bankuna ke bi wajen tabbatar da sahihancin irin waɗannan rahotanni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here