Hassan R Jibrin.
Kawo yanzu, jam’iyyar ADC ta kammala duk wasu shirye-shirye domin gudanar da bikin Canjin shekar Mal. Aminu Ibrahim Ringim, zuwa jam’iyyar hadaka ta ADC.
Magoya baya daga ilahirin fadin jihar Jigawa, ana sa ran yin turururuwar shaida bukin a mazabar sabon dan ADC a garin Ringim.
Bikin zai gudana ne a unguwar Marakawa inda yake zabe.
Sauya shekar shine Karo na uku a tarihin siyasar Aminu Ringim duk hakan ba wani sabon Abu bane ga wasu jiga-jigai a siyasar Najeriya.
Wasu na ganin cewar jagoran na su, gogeggen dan siyasa ne wanda ya shiga fagen siyasa tun a jumhuriya ta biyu ta wakiltar tsohuwar karamar hukumar Ringim a majalisar dokokin tarayya.









