Daga Hassan R Jibrin.
Jami’ar jihar Vernont dake kasar Amurka, ta karrama wata mage mai suna Max, alokacin bukin yaye dalibanta.
Ita dai Max ta samu wanna tagomashin din ne biyo bayan shafe shekaru da dama a cikin jami’ar ba tare da samunta da wani laifi ba,sai dai kasancewarta mai son zaman lafiya tsakaninta da jami’ar.
Digirin girmamawar na zaman lafiya, hakuri da kawar da kai ga duk wasu tsokar nama da sauran makulashe da akai wasarere da su.Jami’ar ta Vermont, tana daga cikin manyan jami’o’i dake kasar ta Amurka wacce ta shafe shekaru masu yawan gaske wajen yaye kwararrun masana a fannoni daban-daban.










