Daga Hassan R Jibrin.

Al’ummomin Karamar Hukumar Dawakin-Kudu dake jihar Kano, sun bukaci matashin dan siyasa kuma hamshakin dan kasuwa, Alhaji Yahaya Muhammad wanda aka fi sani da Yahaya Manaja, da nemi takarar majalisar dokokin jihar Kano a karkashin jam’iyyar hadaka ta ADC a zaben shekarar 2027.

Kiran ya biyo bayan ziyarar bazata da al’ummomin suka kai masa a gidan sa dake garin Gano.

Alhaji Yahaya Manaja, ya gode wa jama’a kan wannan girmamawa da suka nuna masa.

Manaja Ya kuma bukace su da hakuri da juriya a koda yaushe.

“Idan Allah ya tabbatar muku da wannan bukata zan yi kokarin bunkasa tattalin arzikin wannan karamar hukuma ta hanyoyi daban-daban na kasuwancin zamani” a cewar sa.

Magoya bayan na ganin matashin, mutum ne mai tallafawa jama’a na tsawon lokaci kuma samun damar cin zabe a gareshi abu ne mai sauki duba da karbuwar sa a tsakanin al’ummomin Dawakin-Kudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here