Yakubu Uba Muhammad.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya rattaba hannu kan wata muhimmiyar kwangila ta kimanin dala miliyan 1.2 da wani kamfanin gyaran alaƙa a ƙasar United States, a wani yunkuri na ƙarfafa matsayinsa a siyasar duniya.

Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ɗan siyasar ke shirin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027. Ana ganin kwangilar za ta taimaka wajen inganta hotonsa a idon ƙasashen waje da kuma ƙara masa karɓuwa a fagen siyasa na duniya.

Masana harkokin siyasa na bayyana cewa amfani da kamfanonin gyaran alaƙa (PR firms) abu ne da ya zama ruwan dare a siyasar zamani, musamman ga manyan ‘yan takara da ke son ƙara tasiri da martaba a idon duniya.

Sai dai wasu na ganin cewa irin wannan mataki na iya jawo ce-ce-ku-ce, musamman dangane da yawan kuɗin da aka kashe da kuma tasirinsa ga siyasar cikin gida.

A cewar masu sharhi, duk da cewa hakan na iya taimaka wa Atiku Abubakar wajen inganta dangantakarsa da ƙasashen waje, har yanzu babban ƙalubalen da ke gabansa shi ne yadda zai shawo kan matsalolin cikin gida da kuma samun goyon bayan al’ummar Najeriya.

Rahoton ya ƙara da cewa, matakin na iya zama wani ɓangare na dabarun siyasa da ake yi tun kafin a fara zafafa fafatawar zaɓen 2027, inda ake sa ran manyan ‘yan siyasa za su fara shimfiɗa dabarunsu tun da wuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here