Hassan Turaki.

Shugabancin kungiyar wayar da kan al’umar karamar hukumar Gwaram hadin gwiwa da kungiyar magoya bayan Captain Aliyu Muhammad Gadama ne suka yi wannan kira a wani taron manema labarai da ya gudana a sakatariyar Yan Jaridu dake birnin Dutse.

Yayin da yake jawabi a wajen taron shugaban tawagar Kuma tsohon sakataren jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwaram, Hon. Kabiru Muhammad Fagam yace; hadakar kungiyoyin sunyi Shirin tsaf domin tabbatar da nasarar Captain Aliyu Muhammad Gadama da jam’iyyar APC a kowani mataki duba da irin gagarumar gudumawa da yake baiwa alu’mar karamar hukumar Gwaram dama jihar Jigawa.

Fagam ya kara da cewa; Captain Aliyu ya raba wa akalla mutum dubu biyu kayayyakin abinci domin saukaka musu aiwatar da ibadun su cikin nitsuwa. Haka Kuma ya raba wa sama da marayu dubu daya kayan Sallah domin Sanya su cikin al’uma dan aiwatar da bukukuwan Sallah ba tare da maraici ba.

Hon. Kabiru yayi godiya ta musamman ga Captain Muhammad Aliyu a madadin al’umar karamar hukumar Gwaram dangane da yunkurin sa na aiwatar da ayyukan gyare-gyaren matsalar zaizayar kasa Wanda ke lalata hanyar Sara dama hanyar Gadama.

Ya kara da cewa kwarewar sa da kokarin sa na rike al’uma yasa suke neman sa da ya amsa kira domin cigaba da gudanar da ayyukan sa a hukumance.

Da yake amsa tambayar yan jarida dangane da daukan matakin tallata gwanin su tun Kafin fitar da yan takara, Fagam yace suna da kwarin gwiwa dangane da cancantar gwanin su, Kuma suna shirye domin karbar umarnin gwamna lokacin aiwatar da zabukan fidda gwani.

A karshe, Shugaban tawagar kungiyoyin yayi kira ga alu’mar karamar hukumar Gwaram da su bada cikakken hadin Kai da goyon baya dangane da wannan mataki na kira ga Captain, Dr. Muhammad Aliyu Gadama domin ya amince yayi takarar majalissar tarayya me wakiltar karamar hukumar Gwaram a majalissar tarayyar Nigeria a matsayin sa na cikakken Dan kishin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here