Ibrahim A. Makama.
Dan gwagwarmayar siyasa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Hon Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi sani da Dawisun Kanawa, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar (APC) tare da komawar sa sabuwar jam’iyyar (ADC).
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Yakasai ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan gudanar da shawarwari masu zurfi da tuntuba da ‘yan uwa, abokan arziki Ya ƙara da cewa tuni ya mika takardar ficewa daga jam’iyyar APC, tare da kammala rajista a sabuwar jam’iyyar sa ta ADC, wanda hakan ke nuna cikakken sauyin akalar sa a fagen siyasa.
Yakasai ya kuma yi kira ga masu sha’awar shiga jam’iyyar ADC da su yi amfani da damar yin rijista ta yanar gizo cikin sauƙi, yana mai cewa tsarin rajistar yana ba da damar samun katin ɗan jam’iyya cikin kankanin lokaci.
A cewarsa: “Duk wanda ke da sha’awar shiga jam’iyyar ADC zai iya yin rijista ta wayar hannu cikin sauƙi, kuma cikin kankanin lokaci zai samu katin sa na ɗan jam’iyya.
Salihu Tanko Yakasai dai na daga cikin matasa masu tasiri a harkokin siyasa a jihar Kano da ma Arewacin Najeriya, inda ake sa ran wannan sauyin nasa zai iya yin tasiri a fagen siyasar yankin.










