Naziru Hamisu.

Wata sanarwa da matatar ta fitar a shafinta na X ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan saukar farashin danyen mai a kasuwannin duniya kuma an yi hakan ne bisa tsarin sabon farashi da kamfanin ya fitar.

Matatar ta kuma rage farashin man dizal zuwa naira 1,430 kan kowace lita daga tsohon farashin naira 1,620, wanda ke nuna ragin naira 190.Babban jami’in matatar ya jaddada ƙudurinta na taimakawa wajen karfafa tsaron makamashi a Najeriya tare da la’akari da halin tattalin arzikin da ‘yan kasar ke ciki.Wannan shi ne karo na farko da aka rage farashin bayan ƙarin sau uku a jere da aka yi a makonnin baya wanda ya sa farashin man ya yi matukar tashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here