EDITA.

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana rashin amincewarsa da tsarin “consensus” da aka ce jam’iyyar APC ta yi a Jihar Gombe, yana mai cewa tsarin bai haɗa kowa ba kuma ya saɓa wa doka.

A cikin wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed ya fitar a madadin magoya bayan Pantamiyya Movement a ranar Lahadi, an ce Pantami yana Abuja ne lokacin da suka samu labarin abin da suka kira “naɗa sarauta” da aka gabatar a matsayin consensus ga dukkan mukaman zaɓe a jihar.

Sanarwar ta ce, a bisa doka, ba za a iya samun sahihin yarjejeniya (consensus) ba sai an haɗa dukkan ‘yan takarar da suka sayi fom kuma suka kammala cikawa.

“Ba za’a ce an yi consensus mai inganci ba idan ba’a samu yardar dukkan ‘yan takara ba,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta kuma jaddada cewa sashe na 84(2) na dokar zaɓe ta Electoral Act 2022 ya tanadi hanyoyin fitar da ‘yan takara kamar haka:

Consensus: Dole ne dukkan ‘yan takara su amince a rubuce su janye. Idan mutum ɗaya ya ƙi, dole a koma zaɓen fidda gwani kai tsaye.

Zaɓen fidda gwani kai tsaye (Direct primaries): Duk wani ɗan jam’iyya mai rajista yana da damar zaɓar wanda yake so.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan tsarin da aka kira consensus ya saɓa wa doka da kuma umarnin shugabannin jam’iyya na ƙasa, har ma da jagorancin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Duk da haka, an buƙaci magoya baya su kwantar da hankalinsu su ci gaba da bin doka, yayin da aka ce lauyoyin ƙungiyar na duba matakan da za a ɗauka, musamman kan batun rajistar mambobin jam’iyya a jihar.

A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci magoya bayan ta su shirya domin zaɓen fidda gwani kai tsaye idan hakan ya zama dole.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here