Daga: Muhd chamama.

Wani mutum mai suna Bala Adamu, dan asalin garin Kadani a Karamar Hukumar Kura ta Jihar Kano, ya samu hukuncin dauri a gidan gyaran hali bisa zargin hada-hadar sayar da ganyen tabar wiwi.

Kotun ta Majistare ta daya dake Kura, karkashin jagorancin Chief Majistare Muhammad Alh. Isa, ce ta yanke hukuncin bayan wanda ake zargin ya amince da laifin a gaban kotu.

A cewar Insifector Nasiru Abubakar Dan-Sokoto mai gabatar da kara, an kama Bala Adamu kimanin sati uku da suka gabata tare da kayan zargi da suka hada da tulin ganyen tabar wiwi.

Lokacin da aka fara gurfanar da shi a baya, ya musanta laifin. Sai dai a zaman kotun na wannan makon, wanda ake zargin ya daga hannu ya tabbatar wa kotu cewa ya aikata laifin.

Da yake yanke hukuncin, Chief Majistare Muhammad Alh. Isa yace tun da wanda ake zargin ya amince da laifin, kotu ta yanke masa hukuncin Watanni 18 a gidan gyaran hali ba tare da zabin tara ba, bisa zargin mallakar tabar wiwi.

Haka Kuma me shari’ar ya kara masa Watanni 6 a gidan gyaran hali ko tarar Naira dubu 40,000, bisa zargin sayar da tabar wiwi.

Daga nan kotu ta mika shi ga Insifector Zakariya Abdullahi Kurawa na gidan gyaran hali domin aiwatar da hukuncin.

A lokacin da aka fito daga kotu, wakilinmu yayi kokarin yin zantawa da shi, amma hakan ya ci tura.

Hukumar Yan Sanda ta Karamar Hukumar Kura ce ta gurfanar da shi tare da kayan nuni na laifin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here