Daga Hassan R. Jibrin.


Tsohon wakilin Kananan Hukummomin Dawakin-Kudu/Warawa, a Majalisar Dokokin Tarayya, Hon Mustapha Bala Dawaki, ya baiwa wani Masallaci gudunmawar Janareta wanda kudinsa ya kai N150,000 a garin Gano.


Shugaban jam’iyyar NDC na mazabar Gano dake Karamar Hukumar Dawakin-Kudu a jihar Kano, Malam Mika’il Gidan-Kuka, ya sanar da karbar gudunmawar domin mikawa ga Babban Limamin masallacin, Sheik Al Abashir Bn Ilyas Bn Abbas.


Sheik Al Abbas, ya godewa tsohon wakilin bisa ga wannan aikin alherin da ya gabatar. ya kuma roki Allah Subuhanahu wata-Allah da ya shiga cikin lamuran dan siyasar.


Shi dai wannan masallaci yana daukar masu ibada kimanin mutum 150.
A sakon da Hon Mustapha Bala ya aiko, ya bukaci da yin amfani da Janaretan wajen gudanar da Ibadu a cikin natsuwa da kuma fatan Allah ya karbi ayyukan alheri ga masu yin sa.

Shi dai tsohon Mamban ana sa ran zai yi takara a zaben 2027 a karkashin jam’iyyar NDC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here