Hassan Turaki.

Yayin da siyasar Jigawa ke ƙara zafi gabanin zaɓen gwamna na 2027, shugabannin ADC na ƙara jan ra’ayi kan Mallam Aminu Ibrahim Ringim ya zama mataimakin ɗan takar gwamna, Sanata Sabo Muhammad Nakudu.

Dalilin yana bayyane: gogewa, biyayya, da karɓuwa a ƙasa. Ringim tsohon ɗan takar gwamna ne, tsohon ɗan Majalisar Wakilai, tsohon Kwamishinan Aikin Gona, kuma tsohon Shugaban Ma’aikata.

Shekaru kusan 50 yana siyasa, don haka ya san yadda ake lashe zaɓe a Jigawa.Ya taka rawa wajen haɗa kan jam’iyya lokacin fidda gwani na ADC. Masu sharhi na cewa daidaita rikice-rikice da ya yi ne ya ƙarfafa nasar Nakudu.

Ringim ya taɓa tsayawa takara ƙarƙashin PDP da NNPP, ya gina cibiyar siyasa a dukkanin LG 27. Magoya bayansa sun yaba matakin da ya ɗauka na janye kansa domin goyon bayan Nakudu, lamarin da suka kira balaga da biyayya ga jam’iyya.

Ga ADC, zaɓin Ringim ba tausayi ba ne, dabarar siyasa ce. Yana da kwarewa, tasiri, da ikon haɗa kungiyoyi daban-daban. Tikitin Nakudu/Ringim shine mafi ƙarfi da zai iya tsayawa da ‘yan adawa a 2027.

Shugabannin jam’iyyar na cewa idan ADC ta gaza ɗaukar wannan damar, za ta ba wa abokan gaba nasara kyauta. Sako ɗaya ne:

ADC ta zaɓi Ringim, ta rufe kofa, ta tafi neman nasara.

Sa hannu: Mati Ali

matiali94@guaranteemedia

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here