Daga Hassan Turaki.
Shugaban jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a jihar Jigawa Dr. Sani Muhammad Gumel ya tabbatar da cewa babu wani shiri ko mataki da za a dauka a cikin jam’iyyar ba tare da amincewar majalisar zartarwar jam’iyyar ba.
Sani Muhammad ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga jami’an jam’iyyar da ke fadin jihar, inda ya jaddada muhimmancin bin tsarin da kundin tsarin jam’iyyar ya tanada domin samun tafiya mai kyau.
Gumel ya ce duk wani yanke shawara da zai shafi tafiyar jam’iyyar dole ne ya wuce ta majalisar zartarwa, saboda ita ce babbar hukumar da ke da ikon yanke hukunci a matakin jihar.
Ya kara da cewa wannan matsayi na nufin karfafa hadin kai da hana daukar matakai na bangaranci da ka iya raunana ginin jam’iyyar da kuma kawo rudani tsakanin ‘yan jam’iyyar.
A wani bangare na yanke shawarar, majalisar zartarwar jam’iyyar ta amince da gudanar da ganawa da duk wadanda suka fito takara a karkashin tutar jam’iyyar amma ba su yi nasara ba.
Makasudin taron, kamar yadda shugaban ya bayyana, shi ne neman hadin kai da kara karfafa ‘yan jam’iyyar domin su ci gaba da aiki tare wajen cimma manufofin jam’iyyar.
Sannan yayi kira ga majalissar zartarwar da ta sahale wa jam’iyyar domin aiwatar da feshin maganin sauro a fadin jihar, Wanda tuni majalissar zartarwar ta amince ba tare da jinkiri ba.
Shugaban ya kammala da kira ga ‘yan jam’iyyar da su guji yada maganganu da ka iya haifar da sabani, tare da tabbatar da cewa ADC a Jigawa na shirya kanta yadda ya kamata domin fuskantar kalubalen siyasa da ke gaba.










