Daga Hassan R Jibrin.


Mashawarcin Gwamnan jihar Jigawa Kan Ciyar da dalibai a makarantun jihar, Honarabul Murtala Arrow Ringim, yayin kai wata ziyarar bazata a wasu makarantun jihar domin ganin yanayin ciyarwa, ya nuna gamsuwarsa da bin ka’idar gwamnati ajan lamarin.


Honarabul Ringim ya kuma jaddada aniyar gwamnatin Mallam Umar Namadi ta ganin daliban jihar suna samun abinci mai tsafta da gina jiki.


Akalla makarantu goma sha daya ne ya kaiwa samamen gani da Ido, daga cikin makarantun sun hadar da GGSS Mallam Madori, GGASS Kaugama GTC Hadejia da GUSS Hadejia.


Gwamnatin ta Jigawa tana baiwa ciyarwa ga dalibanta kulawa ta musamman domin samar da kyakkyawan yanayi koyon karatu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here