Daga Hassan R Jibrin.

Shugaban darikar Kwankwasiyya kuma jigo a jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya tabo tarihin fahimtar juna a siyasar Najeriya tsakin bangaren kudancin da arewacin Kasa.

A wani jawabi da ya gabatar a wajen taron kasa na jam’iyyar NDC a Abuja.

Acewarsa tun a shekarun 1954 jam’iyyar NEPU karkashin jagorancin Mallam Aminu Kano da NCNC ta Dr Nmandi Azikwe sun hadu domin fafutukar neman ‘yancin kasa daga turawan mulkin mallaja.

A 1960 dangantakar ta sake wanzuwa yayin da a jumhuriya ta biyu Shehu Shagari ya zabo Dr Alex Ekweme a matsayin mataimakinsa domin ciyar da kasa gaba.

Ko a 1983 marigayi Alhaji Abubakar Rimi ya shiga jam’iyyar NPP ta Kudu, a inda yayi takarar gwamnan Kano bayan ficewarsa daga PRP.

Taron na NDCn ya samu halartar jiga-jigan ‘yan-siyasa, kungiyoyin fararen hula da masu rajin kare tsarin dimokaradiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here