Usman labaran.
Matasa Sun Ci Zarafin Daraktan Kamfen Na APC Tanko Rossi Sabo a Kafanchan dake Kudancin Kaduna a arewa maso yammacin Nigeria.
Wasu da ake zargin matasa ne masu fushi sun farmaki Hon. Tanko Rossi Sabo, Daraktan Tuntuɓa da Wayar da Kai na Sanatan APC, Sunday Marshall Katung, a garin Kafanchan da ke Kudancin Kaduna.
Mai ba Sanatan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Midat Joseph, ya fitar da sanarwa inda ya ce ana zargin harin na da nasaba da siyasa.









