Daga Hassan R Jibrin

Jaridar Pulse Nigeria ta nemi afuwar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, kan rahotan da ta wallafa mai alakanta gwamnatin da bada tallafin jajayen Dan kamfan mata a matsayin tallafi.

Idan ba’a manta ba, yayin ziyarar mai dakin Shugaba Bola Tinubu, Sanata Remi Tinubu anga yadda wasu mata suka daga jajayen dan kamfai a yayin da suke lale marhaba ga bakuwar.

Hakan ya jawo zargin cewar, wasu jami’an gwamnatin Kano ne suka dauki nauyin, bayan daga bisani, gwamnati ta barranta kanta daga waccan rashin da’ar.

Malaman addini a jihar sun yi ALLAH wadai da irin halayyar da matan suka nuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here