Naziru Hamisu.

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Gumel a Jihar Jigawa, Hon. Ahmad Rufai Gumel, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).A cikin wata takardar murabus da ya aike wa Shugaban jam’iyyar APC na mazabar Galagamma a Karamar Hukumar Gumel, mai ɗauke da kwanan wata 5 ga Afrilu, 2026, Ahmad Rufai Gumel ya bayyana cewa ya daina kasancewa ɗan jam’iyyar daga ranar da ya rubuta takardar.Hon. Gumel, wanda ya taɓa zama Daraktan yaƙin neman zaɓe na APC a Karamar Hukumar Gumel a zaɓen 2023, sannan kuma Shugaban kafofin sada zumunta na APC a jihohin Arewa maso Yamma, bai bayyana dalilin ficewarsa a cikin takardar ba.Ya gode wa jam’iyyar bisa damar da aka ba shi a baya, inda ya kammala takardar da cewa murabus ɗinsa ya fara aiki nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here