EDITA.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan Naira tiriliyan 68.32 a matsayin kasafin 2026, tare da kara tsawaita wa’adin na 2025.
A cikin kasafin na 2026, an ware Naira tiriliyan 4.799 don kuɗaɗen da doka ta wajabta a ware, da Naira tiriliyan 15.8 don biyan basuka, yayin da Naira tiriliya 15.4 za su tafi wajen tafiyar da gwamnati, sai kuma Naira tiriliyan 32.2 da aka tanada domin ayyukan raya ƙasa.
Gwamnatin ta ce rabon kuɗin na nuna ƙoƙarin inganta tattalin arziƙi da rayuwar al’umma, tare da mayar da hankali kan ayyukan ci gaba.
A cewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, tsawaita kasafin 2025 zai bai wa ma’aikatu damar kammala ayyuka yadda ya kamata.
Tinubu, ya kuma umarci hukumomi su yi amfani da kuɗaɗen bisa gaskiya da tsari, tare da tabbatar da kammala ayyuka a kan lokaci.










