Edita
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai tare da iyalansa sunyi watsi da tayin jirgin gwamnatin tarayya daga shugaba Tinubu na zuwa Kasar Egypt domin dauko gawar mahaifiyar Nasir El rufa’i da ALLAH ya karbi rayuwar ta bayan dogon rashin lafiya.
Wata majiya ta ruwaito cewa iyalan El rufa’i sunce basu bukatar jirgin fadar shugaban ƙasa a yanzu don sun riga da sun samar da nasu jirgin domin kawo gawar zuwa Najeriya Duk da haka sun bayyana Godiya ga fadar shugaban ƙasa kan wannan tayi.










