Hassan R. Jibrin.

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta sanar da al’ummar jihar da ma sauran jama’a cewa ta samu sahihan rahotannin sirri daga Majalisar Tsaro ta Jiha, da ke nuni da cewa wasu mutane na shirin tayar da rikici da haddasa karya doka da oda yayin bukukuwan Sallah mai zuwa.

Gwamnatin ta jaddada cewa duk da ƙudurin da take da shi na inganta da kuma kare al’adun gargajiyar Kano, ba za ta yi wasa da babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata ba na tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Biyo bayan hakan, bayan tattaunawa da Majalisar Masarautar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnati ta amince da waɗannan tsare-tsare na gudanar da bukukuwan Sallah:Hawan Idi (Hawan Sallah):

Za a gudanar da shi karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, daga filin Sallar Idi na Kofar Mata zuwa Gidan Shettima, inda zai kare a Kofar Fatalwa na Fadar Sarkin Kano ta bin hanyoyin da aka tsara.

Hawan Nasarawa:

Za a gudanar da shi ne a wani tsari na musamman, amma ba tare da hawa dawakai ba.

Hawan Daushe:

An dakatar da shi a wannan karon, tare da shirin gudanar da shi a bukukuwan Sallah na gaba Insha Allah.Hawan Fanisau da Hawan Dorayi Su ma an dakatar da su na ɗan lokaci domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron jama’a.

Haka kuma, an umarci dukkan hukumomin tsaro da su ƙara zage dantse wajen sa ido, tare da tabbatar da bin waɗannan umarni, da ɗaukar dukkan matakan doka domin hana duk wata barazana ga zaman lafiya kafin, lokacin da bayan bukukuwan.

Gwamnatin ta kuma buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda, tare da ba hukumomin tsaro cikakken haɗin kai.

Haka zalika, ta gargaɗi jama’a da su guji yaɗa jita-jita marasa tushe, tare da gudanar da harkokin su cikin lumana a lokacin Sallah da bayan ta.

Gwamnatin Jihar Kano ta yaba da ƙwazon da ƙwarewar jami’an tsaro ke nunawa wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki domin ganin an gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana ba tare da wata matsala ba.

A ƙarshe, gwamnatin ta taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar Sallah, tare da yi musu fatan alheri da zaman lafiya.

Guarantee Newspaper ta samo wannan labari ne daga

Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida

18 ga Maris, 2026

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here