Hassan Turaki.
Wasu jami’an tsaro sun kama Malam Abubakar, wanda aka fi sani da Malam Abubakar Low-cost, Limamin Masallacin Low-cost da ke Zaria, jim kaɗan bayan idar da Sallar Magriba a ranar Talata, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida.
Rahotanni daga iyalan Limamin sun tabbatar da cewa wasu jami’an ‘yan sanda ne suka kama shi. Mai ɗakin Limamin ta bayyana cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Malam Abubakar bai dawo gida ba, lamarin da ya jefa iyalansa da mabiyansa cikin fargaba da rashin tabbas.
Sai dai kamun Limamin bai rasa nasaba da rikicin da ya daɗe yana ci gaba tsakanin limamin masallacin tare da magoya bayansa da kuma ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (Izala), rikicin da a halin yanzu yake gaban kotu domin yanke hukunci.
Majiyoyi sun ce bayan an gudanar da zama tsakanin ɓangarorin biyu domin sasanta lamarin, an zargi Limamin da yin kunnen uwar shegu da wasu shawarwari da aka cimma, inda aka ce ya ci gaba da wasu ayyuka da aka dakatar a masallacin har sai kotu ta yanke hukunci.
Idan ba a manta ba, a ranar Talata ne ƙungiyar Izala ta fitar da sanarwar cewa za ta ci gaba da tafsirinta na azumin watan Ramadan a yau Laraba, duk da takaddamar da ke gudana.
Ya zuwa yanzu, hukumomin ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da dalilin kama Limamin. Ana sa ran ɓangarorin da abin ya shafa za su yi karin haske kan lamarin a cikin sa’o’i ko kwanaki masu zuwa.
- Bazzazagiya Online








