BY: EDITOR.

Wata matashiya mai suna Fatima Musa Usman, ’yar asalin Jihar Yobe, ta samu gagarumar nasara bayan ta kammala rubuta Alƙur’ani Mai Tsarki gaba ɗaya da hannunta**.

An bayyana cewa Alƙur’anin da Fatima ta rubuta ya ƙunshi izifai 60, lamarin da ya jawo yabo da addu’o’i daga malamai, iyaye da sauran al’ummar Musulmi.

Wannan nasara ta zama abin alfahari ga iyalanta da kuma al’ummar Jihar Yobe, musamman ganin yadda matashiyar ta sadaukar da lokaci da ƙoƙari wajen rubuta Littafin Allah da hannunta.

Malamai da al’ummar Musulmi sun bayyana hakan a matsayin babbar ni’ima da abin koyi ga sauran matasa, tare da yi mata addu’ar Allah Ya sanya Alƙur’ani ya zama haske da shiriya a rayuwarta.

Allah Ya ƙara mata himma wajen karatu da koyon Alƙur’ani, Ya ba ta ikon fahimtar sa da aiki da koyarwar sa, Ya kuma saka wa iyayen ta da malaman ta da alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here