Daga Hassan R Jibrin.
Shugabar Ma’aikatan Najeriya, Didi Esther Walson-Jack,ta dauki alhakin wanzuwar Ma’aikatar bogin da ake ce-ce-ku-ce akanta wanda Prince Adeniyi ya kirkira da kuma Shugabanta.
Ms Walson-Jack ta ce dogaro da wata wasika da Prince Adeniyi ya aikowa Ofishinata, ba tare da yin la’akari da cewar wasikar ba sahihiya ba ce, hakan yasa daukar matakin ganin tabbatuwar Ma’aikatar. Kan wannan dalilin yasa ya zama dole a gareta ta dauki alhakin wannan balahiri.
Ita dai wannan Ma’aikatar har daukar Ma’aikata. 300 tayi, inda Shugabanta ke yawan ganawa da jami’an diflomasiyya, Ministoci da Shugabanin Majalisun Dokokin Najeriya da sauran manyan Hukummomin Tsaro akan batutuwa daban-daban.
Zargin cin hanci akan Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaba Tinubu ,Femi Gbajamiala ta tada ballin gano balahirar, inda Shugaba Tinubu ya umarci Hukumar Yaki da Cin Hanci ta ICPC ta gudanar da bincike kan zargin da kuma wanzuwar Ma’aikatar.
Wasu na ganin rashin iya gudanar da aiyukan Gwamnati shine makasudin afkuwar ire-iren wadannan lamura, yayin da wasu ke ganin tukuikuyewar da akewa Shugaba Tinubu ya taimaka wajen haifar da hakan.








