EDITA
Shugaban gudanarwa na kamfanin MTN yana samun albashin Naira miliyan 8.5M a kowace rana.
Kamar yadda bincike ya tabbatar da cewa; shi ne ma’aikacin da ya fi kowanne ma’aikaci albashi mai tsoka a fadin Najeriya.
Karl Toriola shi ne shugaban kamfanin MTN wato (CEO) tun daga shekarar 2021.
Ya taba rike manyan mukamai a kamfanonin sadarwa a Turai da Afrika kafin ya dawo Najeriya.
Kafin ya zama CEO, ya kasance Chief Technical Officer (CTO) na MTN Group A karkashin sa, Kamfanin MTN Nigeria ya kara fadada 4G/5G da kuma ayyukan fintech kamar Momo.
Me bincike; Mutawakkil Gambo Doko.










