Hassan Turaki.
Diyar Tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Sani Abacha Mahaifina na ɗaya daga cikin shugabannin Najeriya da aka fi rashin fahimta a tarihinta amma gaskiya shi mutum ne nagari. Zainab Abacha, ‘yar tsohon Shugaban Ƙasa na NajeriyaMahaifina ya taimaka wajen gina tanadin kuɗi domin Najeriya a lokutan tsanani. Duk lokacin da ƙasar ta kusa shiga matsalar kuɗi, waɗannan ajiyoyin da ya adana a ƙasashen waje sukan zama mafita cikin sauƙi.Da ace mahaifina ya fi son jin daɗi, alatu da nuna isa, da ya kashe kuɗin a kan jiragen ruwa masu tsada, jiragen sama na kansa, ko gina manyan otal-otal a Dubai ko Saudiya. Amma bai yi haka ba ya ajiye su ne domin ranakun wahala ga yan Ƙasa. Na tabbata wata rana, ‘yan Najeriya za su fahimci wanene mahaifina da gaske.






