Me magana da yawun hukumar yan sandan jihar Jigawa SP Shi’isu lawan Adam ya tabbatar da cewa hukumar zata cigaba da Sanya ido domin daukan mataki na doka dangane da masu dabi’ar rufe lambar motar su.

Cikin wata sanarwar da shi’isu ya fitar ya ja hankalin mutane masu ta’ammali da ababen hawa dabsu guji rufe lambar su musamman domin kauce wa fushin hukuma.

Shi’isu yace “Ka ja mutuncin kan ka, ka bar lambar motar ka a bude (plate number)”

Sannan ya lissafa nau’in mutane bakwai da doka ta sahale musu rufewa ko boye lambar motar su.

Mutanen da dokar ta sahale musu sun halar da ;

✓ Governor
✓ Dep Governor
✓ Speaker
✓ Chief Judge
✓ Grand Khadi
✓ Royal Highnesses
✓ Service Commanders.

Dafatan ALLAH ya kara kare mu da jihar mu da kasar mu baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here