Hassan Turaki.

Kungiyar mawallafa reshen jihar Jigawa ta jaddada goyon bayan ta ga gwamnan jihar Mal. Umar Namadi kan yadda yake aiwatar da ayyukan raya kasa da gina alu’ma.

Shugaban kungiyar na riko Kamal Ibrahim Miga ne ya bayyana hakan wa manema labarai Jim kadan bayan fitowa daga wani tattaunawa da sukayi da mawallafa da jami’an gwamnatin jihar domin tabbatar da goyon bayan su ga gwamna Namadi da gwamnatin sa.

Da yake gabatar da jawabin sa wa manema labarai a birnin Dutse bayan kammala taron, shugaban kungiyar na riko Kamal yace “Mu bazai yiwu mu kafa gwamnati Kuma mu yake ta ba, ba muyi duk abinda ya dace ganin mun tallata kyawawan ayyukan gwamna dana shugabannin kananan hukumomi da dukkan ayyukan da masu rike da madafun iko na jam’iyyar APC suke yi domin karfafa musu gwiwa.

Kamal ya kara da cewa; yadda jam’iyyar APC take guda daya, haka kungiyar mawallafa take a dunkule ba maganar gida-gida ko rabuwar Kai, munanan a jam’iyyar APC Kuma Muna tare da gwamna Umar Namadi Danmodi dari bisa dari.

Taron wanda ya samu halartar “ya”yan kungiyar daga sassa da dama na jihar an gudanar da shi a G9 Quarters cikin annashuwa da kaunar juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here