IMO: Masu sayar da yaro sun shiga komar yan sanda

EDITA.

Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7.

An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin Zamba da ke Abuja, yayin da ta ukun da ake zargin ma’aikaciyar jinya ce da ta tsere a yanzu.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Henry Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Okoye ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a Owerri, babban birnin jihar a ranar 14 ga watan Afrilu, biyo bayan wani samame da jami’an tsaro suka yi a lokacin da suke ƙoƙarin siyar da yaron kan kuɗi Naira miliyan 2.7.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *