SIYASA: An hana Ganduje Shiga Ofishin APC na Ƙasa a Abuja

HAFSAT JINGAU.

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na nuna cewa an hana tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, shiga ofishin jam’iyyar da ke Abuja a yau.

Har yanzu babu cikakken bayani daga hukumomi kan musabbabin wannan mataki, sai dai lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar APC da ma tsakanin ‘yan kasa gaba ɗaya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *