EDITA.
Jami’in Hisbah Ya Lakadawa Matashiya Dukan Kawo Wuƙa a Katsina
An samu rahoton cin zarafi daga wani jami’in hukumar Hisbah a jihar Katsina, inda ake zargin ya lakadawa wata matashiya mai suna Aisha Musa dukan kawo wuƙa ba tare da bin tsarin doka da oda ba.
Lamarin ya faru ne da ƙarfe 8:00 na dare a ranar Talata, lokacin da Aisha ta ziyarci babban ofishin hukumar Hisbah dake cikin birnin Katsina domin jin dalilin kama kanin ta da hukumar ta yi.
Bayan fara tattaunawa da jami’in Hisbah ɗin mai suna Nafi’u Kwamanda, rahotanni sun ce rikici ya shiga tsakanin su, wanda daga bisani ya rikide zuwa cin zarafi inda ake zargin Kwamanda Nafi’u ya daki Aisha Musa da ƙarfi har taji rauni.
Wakilinmu ya tuntubi shugaban hukumar Hisbah a jihar Katsina, Sheikh Abu Ammar, domin jin ta bakinsa game da lamarin, sai dai bai samu damar samun sa ba, kafin kammala hada wannan rahoto.
A gefe guda, mahaifiyar matashiyar ta bayyana damuwarta tare da neman a bi mata haƙƙin ‘ya’yanta, tana mai cewa: “Ba daidai bane a rika dukan mutane kamar dabbobi ba tare da gudanar da bincike da bin tsarin doka ba.”
Al’umma na ci gaba da bayyana damuwa kan yadda wasu daga cikin jami’an Hisbah ke aiwatar da ayyukansu cikin zalunci da nuna rashin da’a ga hakkokin ɗan Adam.
Za mu ci gaba da bibiyar wannan lamari domin kawo muku sabbin bayanai idan sun taso.
Leave a Reply