BAUCHI: Matemakin gwamna bai mari minista ba …

HASSAN TURAKI.

Mataimakin Gwamnan Bauchi Auwal Jatau Bai Mari Minista Tugga Ba

Tun jiya labari mara tushe yake yawo a kafafen sada zumunta cewa Mataimakin Gwamnan jahar Bauchi Auwal Jatau ya sheƙe Ministan Harkokin wajen Najeriya Yusuf Tugga da mari yayin shiga fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi.

Wannan labarin ba gaskiya bane. Labari ne mara tushe wanda wasu suka ƙirƙira domin wata manufa wacce suka bar wa kansu sani.

Abinda ya faru shine: Yayin da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya isa fadar Sarkin Bauchi, an samu cinkoso, hakan ya haifar turmutsu-tsu wajen shiga zauren fada. Hatta Sarki da Kashim da ƙyar suka shiga cikin fadar daga bisani aka hana kowa shiga.

Wakilin Guarantee media yana fadar maimartaba Sarkin Bauchi lokacin da abin ya faru kuma ya ɗakko dukkan abinda ya wakana. Babu lokacin da Auwal Jatau ya mari Yusuf Tugga, hasali ma tare suka fito daga mota suna hira.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *