2027: Idan kuka sake zaɓen tinubu za kuyi nadama

HASSAN TURAKI.

Idan na bayyana muku yadda Bola Tinubu yake yin ƙulla-ƙulla wajan ganin ya kashe Yankin Arewa To yan Arewa Ba zasu ƙara Zaɓar Bola Tinubu Ba, za kuyi nadamar marawa Tinubu baya a zaben 2027. Inji Dr Hakeem Baba-Ahmed.

Tsohon Mashawarcin Siyasa na Bola Tinubu, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya fito fili yana jan kunnen gwamnati da yin kira ga Arewa.

Tsohon Mashawarcin Siyasa ga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, wanda yayi murabus kwanan nan, kuma babban jigo a kungiyar Northern Elders Forum (NEF), Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa lokaci yana zuwa cikin watanni shida masu zuwa da Arewa za ta bayyana wa duniya irin shugabancin da take bukata da yadda take son tafiyar da al’amuranta a Najeriya.

Dr. Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka watsa kai tsaye, inda ya nuna cewa Arewa ba za ta ci gaba da hakuri da irin yadda ake gallaza mata da kuma nuna bambanci a gwamnatin Tinubu ba. Ya ce akwai abubuwan da idanuwansa suka gani a fadar gwamnatin da idan ya bayyanasu, mutane da dama daga Arewa za suyi nadamar me yasa su marawa Tinubu baya a zaben 2023.

Ya ce, “Idan na ce zan fara bayyanawa Arewa abubuwan da na gani, to za a ga nadama sosai a Arewa.” Ya kara da cewa, duk da cewa mutane da dama sun marawa Tinubu baya da kyakkyawan fata, to hakan bai sauya musu alkibla ba.

A cewarsa, Arewa za ta farka gabanin zaben 2027 domin ta dauki mataki akan makomar kasar, yana mai cewa idan wani yunkuri na damfara ko rashin gaskiya ya sake maimaituwa, to lamarin kasa zai kai inda ba a zata ba.

“Ina sake nanatawa, idan suna tunanin za su yi irin damfarar da suka yi a baya a 2023, to watakila ba za a samu kasar nan kamar yadda take yanzu ba,” inji shi.

A karshe, Dr. Baba-Ahmed ya nuna godiyarsa bisa damar da ya samu na yin hidima, amma yanzu lokaci ne da zai koma ga jama’arsa domin ci gaba da fafutukar kare muradun Arewa.

Jawabin nasa na nuna irin rikicewar siyasa da sabbin tsare-tsaren da ke kunno kai a fagen siyasar Najeriya, musamman ganin yadda Arewa ke kokarin sake nazari kan rawar da take takawa na hadin kan kasa da shugabanci.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *