MUHAMMAD CHAMAMA.
Shugaban jam’iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas yayi kira ga jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da kar ya shigo jam’iyyar APC da kungiyar siyasar sa mai suna Kwankwasiyya.
Abbas ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gabatar a sakatariyar APC ta Kano a yau Juma’a, ya kara da cewar ba ruwan APC da wata ƙungiya ta siyasa cikin jam’iyyar.
Duk da cewa Abbas bai fadi Kwankwasiyya ba, amma a jawabin nasa ya nuna cewa babu wata kungiya ko jam’iyyar siyasa da za’a bari ta shigo cikin APC.
Ya kara da cewa duk masu tururuwar dawowa APC ba za’a ki karbar su ba amma sai sun je mazabun su sun yi rijista.
Ya kuma ce dukkanin shugabannin da ke rike shugabancin jam’iyyar a matakai daban-daban a jihar suna nan akan mukaman su.
” Muna sanar da duk wanda yake son shigowa APC cewa kofar mu a bude take, amma ka sani shigowar ka APC ba zai hana a EFCC da ICPC cigaba da bincikar ka ba”. Inji Abdullahi Abbas
A bangaren Rabiu musa kwankwaso tuni ya nisanta kansa da magoya bayansa daga shiga Jamiyyar APC.
Leave a Reply