2027: Anata Cece-kuce dangane da sabuwar tafiya …

MUHAMMAD CHAMAMA.

Manyan ƴan siyasar Najeriya da ke jagorantar shirin yin haɗaka tsakanin jam’iyyun hamayya domin tunkarar APC a zaɓen 2027, sun mayarwa ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP martani, a kan matsayar da gwamnonin suka ɗauka cewa ba su goyon bayan ƙulla duk wata haɗaka da za ta fitar da su daga PDP.

Gamayyar ƴan adawar da ta haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023 da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da dai sauran ƴan siyasa, ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da ƙulla sabuwar haɗakar siyasa da za ta ceto Najeriya daga mulkin APC.

Ɗaya daga cikin jagororin tafiyar ƙulla sabuwar haɗakar siyasar ta Najeriya kuma tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa mai kula da shiyyar Arewa Maso Yamma, Salihu Lukman ya yi zargin cewa gwamnonin PDPn na sane cewa jam’iyyar su ta yi lalacewar da gyaran ta zai yi wahalar gaske, domin haka suke neman tallafawa jam’iyyar APC mai mulki da zummar ganin ƴan adawa ba su yi nasarar gabatar da ɗan takara mai nagarta ba a zaɓen 2027.

A ranar 20 ga watan Maris Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi da kuma magoya baya su suka sanar da shirin su na ƙulla wata gamayyar siyasa da za ta tunkari APC a zaɓen 2027 mai zuwa.

Sanarwar ta su ta janyo muhawara da tsokaci daga ɓangarori daban-daban.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *