HASSAN TURAKI.
Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da Gwmanatin Najeriya.
Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tugga ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar.
Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary You Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya ba ne, abu ne na Allah. Allah Ne Ya haɗa wannan zumunta ka, babu wanda ya isa ya raba ta.”
Takwaransa na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa nan gaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su gana da shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, a matsayin ci gaban wannan daidaitawa.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka sanya hannu a kai, ta zama, “darasi ga duk wasu ƙasashen duniya, domin yanzu an shiga wani lokaci da ake fama da tashe tashen hankali.
Leave a Reply