HASSAN TURAKI.
Jigo a jam’iyyar NNPP mai alamar littafi, Buba Galadima, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa APC.
Galadima ya ce jam’iyyar NNPP na cigaba da nunawa ƴan Najeriya irin tsarin mulkin da ya dace da nagartaccen shugabanci da take da shi, inda ya ƙara da cewa ƴan siyasa marasa nasara ne kawai ke magana kan zaɓe mai zuwa a tsakiyar wa’adinsu.
Yayin wata hira da jaridar The Guardian, Galadima ya bayyana cewa da ba don alherin Shugaba Bola Tinubu ba, da da wuya a ce mutum irin tsohon gwamnan Kano ya zama shugaban jam’iyya na ƙasa.
Ya kuma jaddada cewa babu wani mutum mai hankali a Kano ko wani yanki na ƙasar da zai yi alfahari da kasancewa a APC ƙarƙashin jagorancin Ganduje, yana mai zargin cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa na amfani da NNPP don samun shahara a kafafen yaɗa labarai.
Leave a Reply