BORNO: Kananan hukumomi 3 boko haram suka kwace

EDITA.

Sanatan mai wakiltar Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa a halin yanzu mayaƙan Boko Haram sun ƙwace yankunan ƙananan hukumomi uku a jihar.

Ali Ndume ya bayyana cewa mayaƙan kungiyar sun kashe fararen hula samada 200 da sojoji 100 a sabbin hare-haren da suka kai a sassan jihar a baya-bayan nan.

A wata zantawar da aya yi da ’yan jarida a ƙarshen mako, Sanatan ya ce mayaƙan Boko Haram sun kai hare-hare 252 a daga watan Nuwamban 2024 zuwa yanzu.

Ya bayyana damuwa game da dawowar munanan ayyukan kungiyar a jihar duk kuwa da kokarin da sojoji da sauran hukumomin tsaro ke yi domin murƙushe su.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *