AJALI: Mutane biyu sun rasa rayukan su …

HASSAN TURAKI.

Mutane biyu ‘yan asalin Jihar Kano sun rasa rayukan su bayan da dutse ya rufe su a wani wajen haƙar ma’adinai da ake yi ba bisa ƙa’ida ba a unguwar Farin-Doki dake ƙaramar hukumar Shiroro, ta Jihar Neja.

Rundunar ‘yan sandan jihar tace mutanen na haƙar ma’adinai cikin dare ne lokacin da wajen ya rufta kansu, yayin da yan sandan da taimakon mazauna yankin suka kai ɗauki, amma sun tarar da sun riga mu gidan gaskiya.

Rundunar ‘yan sandan tace ta fara bincike kan lamarin, kuma ta ja kunnen jama’a da su guji irin wannan aiki da yake barazana ga rayuka, tsaro da tattalin arziƙin jihar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *