Sanarwa Ta Musamman Daga Rundunar ‘Yan sandan Jahar Jigawa.

HASSAN TURAKI.

Ana sanar da duk matasa ‘yan asalin Jahar Jigawa da suka sami nasarar shiga aikin Dan sanda a matsayin (Police Constables) na shekarar 2022/2023.

Da su hallara a babban ofishin yan sanda (police headquarters) da ke Dutse, tun daga yau Juma’ah 11/04/2025 da karfe 5pm zuwa gobe Asabar 12/04/2025 da karfe 9am na safe don kai su inda zasu karbi horo.

Ana bukatar wadannan matasa da su zo da “printout slip” wanda da shi za’a tantance su tare da sanin cewar sun sami aikin.

Sanarwar ta shafi dukkanin wadanda suka sami aikin a fadin Jahar ta Jigawa ba tare da cewa lallai sai ranar da aka ce suyi reporting a training schools ba (12th_19th April, 2025).

Don karin bayani; 08131992027, 08068428984.

Sanarwa daga ofishin hulda da jama’a na ‘yan sanda dake Birnin Dutsen Jahar Jigawa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *