ASO VILLA: Fadar shugaban kasa tayi amai ta lashe …

HASSAN TURAKI.

Fadar Shugaban Ƙasa ta janye jerin Naɗe-naɗen da Kakakin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Sunday Dare, ya wallafa a ranar Laraba, inda ta amince cewa akwai kura-kurai a cikin adadin da aka bayar.

Sunday Dare, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, cewa Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ƴan Arewa 71 da kuma ƴan Kudu 63 a muhimman muƙamai, daga baya ya amince cewa akwai kuskure a cikin rabon da aka bayyana.

A cikin rubutun farko, Dare ya bayyana cewa tarihin Shugaban Ƙasa tun daga lokacin da yake Gwamnan Legas har zuwa yanzu ya nuna cewa shi shugaba ne mara son ƙabilanci, wanda ke fifita cancanta fiye da la’akari da ƙabila ko addini.

Rabon na yanki ya kuma nuna cewa yankin Kudu maso Yamma ya samu Naɗe-naɗe 26, Kudu maso Kudu 21, yayin da Kudu maso Gabas ta samu 16.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *