Politics

PDP: Najeriya ba ta Tinubu da ayarin sa bane

YAKUBU UBA M.

Gwamnoni 11 na jam’iyyar adawa ta PDP karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad sun shigar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ƙara, a gaban Kotun Ƙoli, inda Gwamnonin suka ƙalubalanci ikon da Shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da shi wajen dakatar da wata gwamnatin da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya a jihar rivers.

Da take Jawabi wa manema labarai shugaban kungiyar Sanata Bala yace Babu wani mutum daya da zai mayar da najeriya tasa shi kadai harma yayi ta yiwa doka Karan tsaye.

Gwamna bala yace najeriya ba ta Tinubu fa ayarin sa bane day zamu zuba Ido ana mana tukin ganganci.

Wannan ƙara da gwamnonin suka shigar ta kuma ƙalubalanci ayyana dokar ta-ɓaci da shugaban ya yi a Jihar Ribas.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button