TA’AZIYYA: Gwamna Namadi ya ziyarci Fadar sarki Kano …

ASHIRU GAMBO.

Gwamna Mallam Umar Namadi ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano Alh Abbas Sunusi a gidansa dake Kano, wanda Dansa Shugaban Jamiyyar APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya karbi ta’aziyyar a madadin iyalan Marigayi Galadiman Kano.

Sannan ya mika ta’aziyyarsa ga al’umar jihar ta hannun gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da Mai Martaba sarkin kano Sanusi Lamido Sanusi, duk na rasuwar Galadiman Kano.

Gwamna Namadi ya kai ziyarar dubiya ga Babban Malamin addininin musulunci, Sheik Abdulwahab Abdallah a gidansa dake Birnin Kano.

Yayi adduar Allah ya jikan Galadima, sannan kuma ya bawa Malam lafiya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *