HASSAN TURAKI.
Sanusi Lamido Sanusi Ya Samu Gayyata Daga Rundunar ‘Yan Sanda!
An samu wata takarda mai dauke da gayyata daga rundunar ‘yan sanda zuwa ga Sarkin Kano Na 16 Sanusi Lamido Sanusi, wadda ke kira da ya halarci wani bincike da za a gudanar a Abuja dangane da wata matsala da ta faru a lokacin bukukuwan Sallah a masarautarsa.
Wasikar, wadda ke dauke da kwanan wata 4 ga Afrilu, 2025, ta bayyana cewa za’a gudanar da taron binciken ne a ranar Talata, 8 ga Afrilu, 2025 da karfe 10:00 na safe a Force Intelligence Department, Abuja.
A cewar takardar, an bukaci mai martaba Sanusi Lamido Sanusi da ya bayyana a ofishin ta domin tattaunawa da bayani kan wani abin da ya faru cikin masarautar sa ta Kano yayin gudanar da bukukuwan Sallah. Takardar na dauke da sa hannun CP Olajide Rufus Ibitoye, kwamishinan ‘yan sanda mai kula da sashen leken asiri.
Leave a Reply