HAWAN KANO: yan sanda sun tsare wanda yayi kisa …

ASMA’U ABDULLAHI.

An Kama Wani Dan daba Da Ya Farmaki Tawagar Sarkin Kano ki Sanusi na II, Inda Ya kashe daya daga cikin masu tsaron Lafiyar Sarkin.

Kamar yadda wani ɗan banga dake tsaron lafiyar sarki ya tabbatar wa mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna koyawa cewa, dan daban ya farmaki tawagar Sarki ne.

A cewar sa, bayan saukowa daga Sallah Mai Martaba Sarki yana hanyar komawa gida ne, sai wani ɗan daba ya nufo Sarkin kai tsaye, a tare da shi akwai wuka, lokacin ina kusa da Sarki na ga ya nufo mu.

Ganin yana kokarin ƙarasowa inda Maimartaba yake nayi sauri na tare shi ya dauko wuka ya caka mun a ciki be samu yadda yake so ba sai wani dan banga yazo, ya buga wa dan bangan wuka ya kashe shi nan take.

Yanzu haka dai dan daban da ya afkawa tawagar Sarkin Kano mai suna Usman Sagiru yana hannun rundunar yan sanda ta jihar Kano yayin da ake cigaba da binciken kwakwaf.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *