IBRAHIM ADAMU DUTSE.
Gwamnatin jihar Edo da ke kudancin Najeriya ta yi Allah wadai da kashe wasu matafiya da aka yi a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Arewa Maso Gabashin Esan ranar Alhamis, inda yaci alwashin hukunta “masu laifin”.
Wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga kudanci zuwa arewacin Najeriya.
Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mutanen da aka kashe ‘yan asalin jihar Kano ne kusan 16.
“Yan sa-kai sun tare matafiyan, suka fito da su daga motarsu, suka yi musu duka, sannan suka cinna musu wuta,” a cewar wani saƙo da Amnesty ta wallafa a shafukan sada zumunta.
Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na jihar Rivers suka ratso ta garin, sai ƴanbanga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne,” kamar yadda sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Fred Itua, ya bayyana.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana adadin mutanen da aka kashe ba a harin, amma ta ce Gwamna Okpebholo ya ziyarci garin a ranar Juma’a, inda ya yi alƙawarin gano waɗanda suke da hannu domin su fuskanci hukunci.
Amnesty ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar an hukunta masu hannu a cikinsa.
Leave a Reply