HASSAN TURAKI.
Dayake kaddamar da tallafin shugaban Karamar Hukumar Jahun Hon Jamilu Muhammad Danmalam yace Hakan na Daya daga cikin manufofin gwamna Mal. Umar A. Namadi fca. Na bunkasa noman Rani Dana damina Dan kawar da yunwa da Samar da abinci ga Al’umma.
Hon Danmalam yace yanzu haka karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara Dan fara noman Rani a karo na farko Dan fadada harkar noman Rani a kan Tudu, yayin da aka zabi kauyen tunubu dake mazaba kanwa Dan fara noman Rani.
An dai gudanar da bikin kaddamar da rabon tallafin kayan noman a garin darai dake mazabar gunka a karamar Hukumar Jahun.
Shugaban karamar Hukumar Jahun Hon Jamilu Muhammad Danmalam ya Kara da cewa wadanda suka anfana da tallafin zasuci moriyar kaso sattin cikin Dari 60% yayin dazasu dawowa da gwamnati kaso arba’in kacal 40%
Kayan tallafin da’aka raba sun Hadar da
- Injin ban Ruwa
- Takin zamani buhu bajwai 7.
- Irin shuka na shinkafa buhu Daya.
- Injin feshi.
- Maganin kwarai
Da sauran kayan aikin gona.
A nasa jawabin coordinator Mai kula da noman Rani Mal suraja Dahiru ya yaba da kokarin shugaban karamar Hukumar Jahun a kokarin dayayi na fadada harkar noman a fadin karamar hukumar, inda yace gwamnatin Jihar Jigawa ta bada umarnin baiwa matasa filin noma a kalla kadsda Dari 100. A dukkannin kananan hukumomin Jihar Jigawa, Amma shugaban karamar Hukumar Jahun ne kadai ya jara adadin filin noma inda sama da mutane Dari uku 300 zasu anfana.
Taron yasami halartar hakimai, digatai, MANOMA ‘yan siyasa da sauran Al’umma.
Isma’il Bature jahun
Me baiwa shugaban karamar hukumar jahun shawara a fannin sadarwa.
Leave a Reply