ASHIRU GAMBO.
Mai Girma Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi FCA, ya gabatar da buɗe baki (Iftar) da Masu bashi shawara da sauran hadiman sa Wanda ya gudana a babban dakin taro dake gidan Gwamnatin jihar Jigawa.
Wannan ba shine karo na farko ba da gwamnan ya gabatar da buɗe baki da jami’an gwamnatin a wannan wata Mai alfarma, domin kuwa Gwamna Malam Umar Namadi ya gabatar da buɗe baki da Kwamishinoni, da Yan majalisar Dokoki ta Jiha da shugabannin Ma’aikatu da hukumomin Gwamnati da daidaikun mutane.
Buɗe bakin ya samu halartar Masu baiwa Gwamna Shawara na Musamman a fanni daban daban, da Mataimaka na Musamman a bangarori daban daban, da sauran mukarraban gwamnati.
Muhammad Isma’il
Leave a Reply