KANO: Gwamna Abba sanar da ɗaukan aiki kai tsaye …

Ashiru Gambo.

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da daukar aiki kai-tsaye ga daliban jihar Kano da suka kammala karatun Digirinsu na biyu a kasar India.

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin liyafar buda baki da daliban su 53 Jim kadan bayan isowarsu gida Nigeria.

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya ce gwamnati zata bawa daliban takardunsu na naukar aiki yace dukkanin gwamnati tana da bukatarsu musamman kasancewar mafi yawansu sun karanta fannonin kiwon lafiya, yace nan bada jimawa ba za a tura au asibitoci daban daban domin fara aiwatar da aiki.

Ya ja hankalin daliban, da su saka wannan abin Alkhairi da aka yi musu ta hanyar tsayawa su yi aiki a jihar Kano kasancewar dukiyar al’umar jihar aka diba aka biya musu har suka Kai ga matsayin da suka cimma a yanzu.

Ya kuma yabawa daliban bisa kwazo da jajircewa da suka nuna wanda ya kaisu ga samun kyakkyawan sakamako abin alfahari ga dukkanin al’umar jihar Kano.

Kazalika gwamnan ya gwangwaje daliban da kudi Naira 100,000 kowannensu.

Daliban wanda dukkanin su sun kammala Digirinsu na biyu a Jami’ar Symbiosis dake Kasar India sun bayyana godiyarsu bisa tagomashin da gwamnan ya yi musu kamar haka.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *