EDITA.
Gwamnan jihar Kano ya bawa sarakuna Umarnin shirye-shiryen hawan Sallah.
Gwamna Engr Abba Kabir Yusuf na Kano ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook Yana Mai cewa Da yammacin yau, na karbi bakuncin manyan Sarakunanmu karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wajen taron buda baki na watan Ramadan, a gidan gwamnati dake Kano, ranar Talata.
A yayin wannan bu’da baki na umarci daukacin masarautun Kano guda hudu da su fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan hawan Sallah Durbar domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan.
Na jaddada cewa, al’ummar jihar suna ɗokin ganin al’adar sanya sabbin tufafi a ranar Sallah, tare da yin jerin gwano a kan tituna domin shaida wa sarakunansu bisa doki, tare da yin musabaha.
Bugu da kari, na bayyana cewa wannan gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba, kuma ba za ta bari duk wasu makiya su tauye wa ‘yan kasa wannan hakki mai daraja ba.
Na kuma tabbatar wa jama’a cewa dukkan hukumomin tsaro a jihar za su ba da himma wajen bayar da kariya ga jama’a a yayin bikin.
Hakazalika, na kuma bayyana cewa za a kaddamar da Majalisar Masarautar Jihar Kano a cikin watan Afrilu na wannan shekara domin samun damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
A yayin da nake nuna jin dadi na kan goyon bayan da suke yi da shugabancin, na yaba wa Sarakunan bisa irin kyakkyawar alaka da suka nuna tun bayan nada su, tare da lura da cewa wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar da ake samun kwakkwarar daraja a tsakanin sarakuna musamman ta fuskar matsayi. – AKY
Leave a Reply